Assalamu Alaikum Abu Aisha, Allah ƙara basira da ƙwazo a wannan hidima ta jama'a. Gaskiya wasu abubuwan da kake faɗa game da Ganduje, akwai matsala a wannan lamarin. Gaduje yayi aikin a cikin Kano babu shakka, amma fa bai kula da karkara ba wajen aikace aikace sa. Don Allah ka samu bayanai game da ayyukan Ganduje zaka tarar cewa duk da shi ɗan ƙauye ne amma bai yi adalci wajen gyara garuruwa da ƙauyuka bayan cikin Birnin Kano. Da ace har yanzu shine shugaban APC na ƙasa da zaka yi mamaki irin yadda zai shige gaba babu ƙaƙƙautawa wajen tallan Tinubu. Ganduje yana cikin yan' siyasarmu na Arewa marasa kishin talakawa da tausayi. Ko a Kano wasu taimako ga yayan talakawa wajen karatu Ganduje duk sai yayi watsi da su, babu kula da asibitocin gwamnati, haka makarantu Ganduje ya ƙi kula dasu ana cunkusa yara a ajijuwa, babu kula malaman makararantun gwamnati dadai sauran abubuwan na rashin adalci, babu kula da bada haƙƙoƙin ma'aikatan gwamnati da yan fansho duk a lokacin Ganduje yana gwamna. Kana iya yin bincike idan kana shakka akan abubuwan da na kawo anan. Shawara ta itace musa abunda yake gaban mu na wayar da kai game da kayar da Tinubu a zaɓe mai zuwa na 2027. Mu bar maganar kawo misalin Ganduje a matsayin gwamnan da za'a ce ya kawo cigaba a Kano idan banda gadoji da wasu gyare gyare a cikin garin Kano.
Shawara ta itace musa abunda yake gaban mu na wayar da kai game da kayar da Tinubu a zaɓe mai zuwa na 2027.
Mu bar maganar kawo misalin Ganduje a matsayin gwamnan da za'a ce ya kawo cigaba a Kano idan banda gadoji da wasu gyare gyare a cikin garin Kano.